Sulaiman20Ibn20Hujjah 2
Barka20Da20Zuwa
Shafi20Mai20Albarka



¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

Zaka iya kiran wayata tanan
HomeBlogAbout MeBayani Akan AZUMIAikin Hajji da UmaraMa anar Shi aAbin da Aka HanaSamun FalalaKasuwanci Mai RibaMahimmancin Addu o iBayanin ZakkaSALLAMATA A MUSULUNCITSARKITAUHEEDI DA AQIDAAYYUKAN ZUCIYAMAHIMMANCIN DA AWATAMBAYA DA AMSASheikh jafar mahmud AdamWadansu websides


SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH


Sheik Lawan Abubakar Gadon Kaya tafseer2017



02/05/24
FB Pantami


Ibn20Hujjah
Source: Google news
0Mozilla/5.0




SULAIMAN Ibn Hujjah

* No categories

Online: Guests: 1


Sulaiman20 FaceBook


HAJJI DA UMRA
**Hajji da umra yana wajaba sau daya a rayuwa, kuma sharuddan wajibcin su sune**
(1) Musulunci
(2) Hankali
(3) Balaga
(4) 'yanci
(5) Ikon zuwa:- shine mutum ya sami guzurinsa da abin hawansa. Wanda ya kubuce masa har ya mutu sai a fitar daga dukiyarsa (a fitar da kudin) hajjinsa da umra a ba wa wani mutum da ya taba aikin don yayi masa.
Kuma baya inganta ga kafiri ko mahaukaci, kuma yana inganta ga karamin yaro ko bawa. kuma baya isar musu daga hajjin musulunci.
Wanda bashi da iko kamar fakiri da zai ci bashi ya yi to da hajjinsa ya inganta.

YIN HARAMA:- Sunna ce ga wanda zai yi harama yayi wanka , kuma ya tsaftata kuma ya sanya turare (a jikinsa kawai), Sa'annan yayi yagusar da kewayayyen abu, kuma ya sanya gyauto da mayafi farare masu tsafta.
Sannan sai ya yi harama da fadar: LABBAIKA ALLAHUMMA UMRA/ HAJJAN: ( Amsa warka ya ubangiji da umrah ko hajji) ko hajji da umrah,
Idan ya na tsoro zai iya sanya sharadin cewa: idan wani mai katsewa ya katseni to zan tsaya daga inda na katse.
Kuma alhaji yana da zabi cikin ayyuka guda uku:
(1) Tamattu'i ( Hajji da umra da hutu a tsakanin su).

(2) IFRADI (hajji kadai)
(3) KIRANI (hajji da umra a hade)
Mafifici a cikin su shine TAMATTU'I.

*TAMATTU'I :- Shine yin harama da watannin hajji, kuma ya cika shi, sannan kuma ya yi harama da hajji a cikin shekarar.
*SHI KUMA IFRADI :- Shine yin harama da hajji kadai.
*SHI KUMA KIRANI :- Shine yin harama da duka biyu, ko kuma yayi harama da umra, amma kafin yayi dawafi sai ya shigar da hajjinsa.
Idan mai nufin hajji ya dai daita akan abin hawansa sai ya yi talbiyya yana mai cewa:-
LABBAIKA ALLA'HUMMA LABBAIKA, LABBAIKA LA' SHARIKA LAKA LABBAIKA, INNAL HAMDA WANNI IMATA LAKA WAL- MULKA, LA'SHARIKA LAKA.
Ma'anar sa : " Na amsa maka ya ubangiji, na amsa maka, na amsa maka babu wani abokin tarayya a gare ka, na amsa maka, lallai godiya da ni'ima da mulki duk suna gare ka, babu abokin tarayya tare da kai".
Kuma ana so a yawaita fadar hakan, da kuma daga murya, amma mata ba za su daga murya ba.

**ABUBUWAN DA AKA HANA MAI IHRAMI YINSU**
(1) Aske gashi (gashin kai, ko na hammata ko na mara).
(2) Yanke farce
(3) Sanya kewayayyen abu ga namiji, sai dai idan bai sami gyauto ba sai ya saka wando, ko idan bai samo silifas ba sai ya sanya khuffi, kuma babu fansa a kansu.
(4) Rufe kai ga namiji
(5) Sanya turare a jiki ko tufafi
(6) Kashe abin farauta. shine dabbar daji da ta halatta.
(7) Daura aure, haramun ne, amma babu fansa a kansa.
(8) Runguma domin sha'awa da abinda bai kai farji ba, fansar shi, shine yanka akuya ko azumin kwanaki uku ko ciyar da miskinai shida.
(9) Saduwa ta farji, idan ya kasance kafin jifan farko ne to hajjinsa ya baci.
Kuma dole ya cika shi kuma ya rama shi wata shekara, tare da yanka rakumi ya raba wa talakawan garin makka.
Idan kuma bayan jifan farko ne hajjinsa bai baci ba, sai dai dole ya bada jini idan ya sadu da mace a cikin umra ta ya bata ta kuma zai yanka akuya kuma dole ya rama ta.

Hajji ko umra ba su baci da wanin jima'i, kuma mace kamar namiji take sai dai ita za ta iya sanya kewayayyen abu kuma zata sanya abin da zai rufe ido ba nikabi ko safar hunnu ba.

**FIDYA** Kashi biyu ne:
{1} Fidiyar da aka bada zabi cikinta; Kashi biyar ce, fidiya aski ko turare ko yanke farce ko rufe kai, ko sanya kewayayyen abu ga maza, sai ya yi zabi tsakanin azumin kwana uku ko ciyar da miskinai shida ga kowa ne miskini rabin sa'i (1/2), Ko yanka akuya.
Kuma sakamakon farauta misalin abinda ya kashe daga dabbobin gida idan akwai makamancinsa, idan babu kamansa sai a kimanta a fitar.
(2) Kaso na biyu kuwa ajere: shine fidiyar mai tamattu'i da kirani ta hanyar yanka akuya, da kuma fansar jima'i wadda shi ne; rakuma.
Idan kuma bai samu ba sai ya yi azumin kwana uku a hajji, bawai kuma bayan ya dawo gida.
Shi kuma hadaya ko ciyarwa ba sa kasancewa sai talakawan da suke cikin haramin Makkah.

**SHIGA MAKKA**
Idan alhaji ya shiga masallacin harami sai ya yi zikirin da aka shar'anta yayin shiga masallaci, sannan ya fara dawafin umra idan tamatu'i zai yi.
ko yayi dawafin isa makka idan ifradi ko kirani zai yi. sai ya nada mayafinsa ya sanya tsakiyansa kasan kafadarsa na dama, gefen ihramin kuma a kafadar hagu, zai fara daga hajarul- aswad, ya shafo shi ya sumbace shi, ko yayi nuni a gareshi, kuma yace (bismillahi, wallahu akbar). zai aikata haka a kowane zagaye, sannan ya sanya dakin Allah a hagunsa, yayi dawafi guda bakwai. yana sassarfa, azagaye na uku na farko gwargwadon iyawa, sai yayi tafiya a sauran zagayen, duk sanda ya zo daidai rukunul- yamani sai ya taba shi, idan da hali. yana mai fadan wannan addu'ar a tsakanin rukunnan:
RABBANA' A'TINA' FID-DUNYA HASANATAN WA FIL- A'KHIRATI HASANATAN WA QINA' AZA'BAN-NA'RI.
Ma'anarsa: " Ya Ubangijimu! Kaba mu kyakkyawa a duniya, kuma ka bamu kyakkyawa a lahira, ka kuma tsare mu daga azabar wuta". (suratul Baqara - Aya ta 201)


{{SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH A SAUKAKE }}
Kuma a sauran kewayensa ana so ya yi ta yin addu'an da duk ya ke so. sannan ya yi salla raka'a biyu a bayan mukamu ibrahim -in ya yiwu-. yana mai karanta suratul kafirun da ikhlas.
Sannan sai ya sha ruwan zam-zam kuma ya sha da yawa, sai ya koma zuwa hajarul- aswad ya taba shi -idan da hali- sannan yayi addu'a a multazam (tsakanin hajarul- aswad da kofa)' sannan sai ya fita zuwa safa yana mai tsayawa a kai; yace: "Ina farawa da abin da Allah ya fara da shi". Sai ya karanta fadarsa madaukaki:
INNAS-SAFA' WAL-MARWATA MIN SHA'A'RIL-LA'HI FAMAN HAJJAL BAITA AWI'ITAMARA FALA JUNAHA ALAIHI AN YADDAWWAFA BIHIMA' WAMAN TADAWWA'A KHAIRAN FA INNAL LAHA SHA'KIRUN ALIMUN.
Ma' ana sa: "Lallai ne safa da marwa suna da wuraren ibadar Allah to wanda yazo hajjin daki ko umra, to babu laifi a kansa ya yi dawafi gare su (biyun), kuma wanda ya kara yin wani aikin alheri to lallai Allah mai godiya ne, masani" (suratul Bakara - aya ta 158).

Kuma sai yayi takbiri yayi hailala, kuma ya fuskanci ka'aba, ya daga hannunsa yana mai addu'a, sannan ya sauka ya tafi zuwa koriyar alama, sannan yayi sauri har zuwa daya alamar, sannan ya tafi har sai ya zo Marwa, sai ya aikata irin abin da ya aikata a safa, (banda karanta ayar) sannan ya sauko sai ya aikata abin da ya aikata a zagayen farko har sai ya gama zagaya bakwai. Daga safa zuwa marwa zagaye daya kenan, daga marwa kuma zuwa safa shi ma zagaye daya ne.
Da haka har ya gama, sannan sai ya yi saisaye ko aski amma anfi so yayi aski sai dai mai umrar Tamattu'i; domin zai yi hajji a bayanta.
Amman kirani ko ifradi shi ba zai yi tahlili bayan dawafin isa dakin Allah ba, har sai yayi jifa ranar idi jifan farko.
Hukuncin mace kuma cikin ayyukan hajji kamar na namiji ya ke, sai dai ita ba ta sassarfa wurin dawafi ko wurin sa'ayi.

**YADDA AIKIN HAJJI YAKE**
Idan ranar tarwiyya (takwas ga watan 12) tayi, sai wadda da ya kasance ya waraware haramarsa (da ya gama umra) sai yayi harama daga gidansa (masaukin alhaji) a makka; Sa'annan ya nufi mina domin yayi kwanan daren tara ga wata.
Idan rana ta bullo a hantsin ranar tara ga wata sai ya wuce zuwa arfa, sannan idan rana ta kauce sai yayi sallar azahar da la'asar jam'i kuma kasaru .
Kuma arfa duk wurin tsayuwa ne sai dai wani fili ( kwarin urana), kuma zai yawai fadar:
LA'ILA'HA ILLALLA'HU WAHDAHU LA SHARIKA LAHU LAHUL MULKU WA LAHUL HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR
Ma'anarsa: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma mulki yana gare shi, godiya tana gare shi, kuma shi mai iko ne akan komai".

Kuma sai ya dage da addu'a da tuba da kwadayi wurin ubangiji. To idan rana ta fadi sai ya nufi muzdalifa cikin nutsuwa da kankan da kai, yana talbiyya yana ambaton ubangiji.
Idan ya isa muzdalifa sai yayi sallar magariba da isha'i jam'i kuma kasaru (ga sallar isha' kadai; saboda magariba ba a mata kasaru). Sannan ya kwana a wurin, sannan yayi sallar Asuba a farkon lokacinta.
Kuma ya zauna ya na addu'a har sai gari yayi haske kafin rana ta fito.
Sannan ya wuce, idan ya isa kwarin (muhassar) sai yayi sauri sosai -idan ya samu iko- ( yana ta tafiya) da haka har ya isa mina, sai yayi jifa ( jamratul akbah) sai ya jefe ta sau bakwai kamar tsakuwar ferawa (tsakanin dogon yatsa da babba), girmansa kuma kamar gujiya da gyada, yana mai yin kabbara wurin kowane jifa, kuma zai daga hannayensa wurin jifan.

Sharadi ne kuma tsakuwar ta fada cikin kwarin (wannan kewayen), koda ba ta doki matsayar ba (ginin da ke tsaye).
Yana yanke talbiyya da fara jifa, sannan ya yanka hadayarsa, sai ya aske gashi ko yayi saisaye amma anfi so yayi askin, kuma da jifa ne komai ya ke halatta a gare shi in banda mata.
Wannan shine tahallulin farko (wato: warwarewan farko).
Sannan ya wuce makka don yayi dawafi (ifada) shine dawafin dole, wanda saida shi hajji ke cika, sannan yayi sa'ayi tsakanin safa da marwa idan mai tamattu'i ne ko idan bai yi sa'ayi ba tare da dawafin isowa dakin (kudumi).
Idan yayi wannan komai ya halatta a gare shi har da mata.
Wannan shine tahalluli na biyu. sannan sai ya koma zuwa gida (mina) don ya kwana dararenta guda biyu ko uku, wannan kwanan wajibine (wato: ranakun sha daya da sha biyu),

Sai kuma ya jefi wuraren jifansu guda uku bayan rana ta yi zawali ( a wadannan ranakun za a jefi dukkan wuraren jifa guda uku ne, sabanin ranar goma) kowace za a jefe ta da tsakuwa bakwai, zai kuma fara ne daga jifan farko da tsakuwa bakwai, sannan ya gabata ya tsaya yayi addu'a (wato ya roki Allah bukatunsa).
Sannan ya zo ta tsakiya ya jefe ta kamar yadda yaxi ta farko. yayi addu'a bayanta sannan ya jefi (jamratul akba) amma ita kam ba zai tsaya wurin ta ba. Sannan a rana ta biyu ma yayi jifa kamar yadda yayi.
Idan ya so ya gaggauta sai ya fita kafin faduwar rana.
Amma idan har rana ta fadi masa alhali bai fita daga mina ba (wato: ranar sha biyu ga wata) to dole ya tsaya yayi jifa gobe, sai dai idan cunkoso ne ya rike shi ya hana shi fitan ga shi kuma yayi azamar (niyyar) fita to babu laifi ya fita ko bayan faduwar rana ne.

Mai Kirani kamar mai ifradi ne sai dai shi hadaya ta wajaba akansa kamar mai tamattu'i.
Idan yayi niyyar tafiya zuwa wajen iyalinsa ba zai fita ba sai yayi bankwana da dakin Allah da dawafi domin ya zama karshen lokacinsa da dakin ne, sai dai mai haila ko nifasi dawafin bankwanan ya fadi a kansu.
Idan kuma bayan yayi dawafin sai ya shagalta da kasuwanci kafin ya fita to dole ya sake shi. Mutumin kuma da ya fita baiyi shi ba, in ya kasance a kusa yake to dole sai ya dawo.
Idan kuma yana nesa ne to sai ya bayar da jini.

**RUKUNNAN HAJJI GUDA HUDU NE**
(1) Yin harama: shine niyyar shiga cikin aikin hajji.
(2) Tsayuwar Arfa.
(3) Dawafin ziyara (ifada)
(4) Yin sa'ayin hajji.

**ABUBUWAN DA SUKE WAJIBI A HAJJI TAKWAS NE**
(1) Yin harama daga mikati.
(2) Tsayuwar arfa har zuwa dare.
(3) Zaman muzdalifa har zuwa bayan rabin dare.
(4) Zaman mina a dararen ranaku biyu ko uku bayan salla (wato: 11 da 12 da 13 na watan 12).
(5) Yin jifan shaidan.
(6) Aski ko saisaye
(7) Dawafin bankwana.
(8) Yanka ga mai hajjin tamatu'i ko kirani.
**KUMA RUKUNNAN UMRA UKU NE**
(1) Yin harama.
(2) Dawafin umra.
(3) Sa'a yin umra.
**WAJIBAN UMRA GUDA BIYU NE**
(1) Yin harama daga mikati.
(2) Aski ko saisaye.
Wanda ya bar wani rukunin, aikin shi baya cika sai da shi. Wanda kuma ya bar wani wajibi: to dole ya bayar da jini. wanda kuma yabar wata sunna to babu komai a gare shi.

**SHARUDDAN INGANCIN DAWAFI GOMA SHA UKU NE**
(1) Musulunci
(2) Hankali
(3) Niyyar da aka ayyana
(4) Shigar lokacin dawafi
(5) Rufe al'aura ga mai iko
(6) Tsarki daga wani hadasi ba ga yaro ba.
(7) Tabbatarwa da cikarsu kewaye bakwai
(8) Sanya ka'aba a hagun, tare da kuma sake abin da yayi kuskure a cikinsa
(9) Rashin dawowa ta wurin tafiya
(10) Yin tafiya ga wanda zai iya
(11) Bibiya tsakanin ayyuka
(12) Kuma ya zama a cikin masallacin Harami
(13) Sa'annan kuma ya zama an fara daga Hajarul-aswad.

**SUNNONIN DAWAFI**
Taba hajarul-aswad da sumbantarsa, da yin kabbara a wurinsa, da sumbatar Rukunul-yamani, da fito da kafada da sassarfa ko tafiya awurin yinsu( wato kewaye ukun farko na dawafi), da yin addu'a da ambaton Allah aya yin dawafin, da kusantar dakin Allah, da yin raka'oi biyu bayan dawafi a Mukamu Ibrahim.

**SHARUDDAN SA'AYI GUDA TARA NE**
(1) Musulunci
(2) Hankali
(3) Yin niyya
(4) Bibiya
(5) Yin tafiya ga wanda zai iya
(6) Cika bakwai
(7) Kammalawa tsakanin Safa da Marwa
(8) Kasancewarsa (safa da marwa) bayan dawafi ingantacce.
(9) Fara shi daga safa da cika shi a marwa.

**SUNNONIN SA'AYI**
Tsarkaka daga hadasi ko khabasi, da sitirta al'aura, da zikiri da addu'a yayin yinsa, da yin sauri ko tafiya a wurinsa, da hawa kan duwatsun safa da marwa, da kuma bibiya tsakanin shi da dawafi.

Abin da yafi kyau shine yin jifa a rana guda, Amma da mutum zai jinkirta jifan yau zuwa gobe ko sauran ranakun tashriki to ya isar masa.

**YIN LAYYA**
Sunnace mai karfi, idan goma ga zul-hijja ya shiga,
haramun ne ga wanda zai yi layya ya yanke wani abu daga gashinsa ko farcensa ko fatarsa har sai ya yanka abin layyarsa.

**YANKAN SUNA**
Sunnace shi ne a yanka wa namija rago biyu ga mace guda daya.
Ana yanka wa a rana ta bakwai amma yadda aka fi so, kuma sunna ce a aske kansa ayi sadakar azurfa da dai dai nauyin gashin.
A kuma sa masa suna a wannan ranar (bakwai, ko kafinsa), mafi sayowan suna a wajen Allah shine Abdullahi, da Abdurrahman.
Idan layya ya hadu da abin suna to daya daga cikinsu ta wadatar a madadin dayan.

ALHAMDULILLAH.

WANNAN SHINE BAYANIN HAJJI DA UMRA
Sulaiman20Ibn20Hujjah-1 2

The Soda Pop